ABNA24 : Malam Ouhoumoudou, mamba ne a jam’iyyar PNDS-tarayya na kusan shekaru talatin, kana kuma daya daga cikin makusantan tsohon shugaban kasar Alhaji Issoufou Mahammadu.
Dan shekara 66, masanin tattalin arziki, ya taba rike mukamin ministan ma’adinai da makamashi 1991 zuwa 1993 sai kuma ministan kudi tsakanin 2011 zuwa 2012.
A 2015 aka nada shi shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa.
Dan asalin jihar Tahoua, kuma makusancin tsohon shugaban kasa Issoufou Mahammadu, yana da masaniya sosai akan manyan ayyukan gwamnatin data shude.
Masana na ganin zabensa bai zo da mamaki ba, kasacewarsa na hannun daman tsohon shugaba Issoufou, kana kuma wanda jiharsa ta kawo kuri’u kusan miliyan daya, wanda suka baiwa Malam Bazoum Mohamed, samun nasara a zaben shugabancin kasar.
342/